Biyo bayan halin kuncin da ake fama da shi na cire tallafin man fetur, gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Yusuf ya amince da warware basussukan da hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO ta ke bin jihar,Daily Post ta rawaito.
Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta shafin sa na Twitter.
KARANTA WANNAN: Iyakokin Arewa Yanzu Sun Koma Matattarar Fataucin Bil-Adama – NAPTIP
A cewarsa, an yanke shawarar ne don baiwa dalibai 55,000 na makarantun gwamnati damar zana jarabawar kammala makarantun sakandare SSCE na shekarar 2023.
“A wani bangare na kudirin gwamnatinmu na sake mayar da bangaren ilimi ta hanyar ba su damar shiga tsakani da ake bukata.
“Na amince da gaggauta daidaita kudaden da hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta ke bin jihar domin baiwa dalibai 55,000 na makarantun gwamnati damar shiga rubuta jarabawa SSCE 2023”. ya rubuta.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa a shekarar 2022 ne hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta sha alwashin hana daliban Kano rubuta jarabawar kan bashin da take bin jihar na tsabar kudi naira biliyan 1.5.
An shirya fara rubuta jarabawar NECO a ranar 27 ga watan Yuni 2023.
A wani labarin kuma, Cancanci Zama Gwamna, Kwankwaso Ya Fadawa Dan Takarar NNPP
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya yi kira ga dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Imo, Ben Odunze, da ya tabbatar da manufar jam’iyyar gabanin zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Kwankwaso, a cewar wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Joshua Elekwachi, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da ya ziyarci dan takarar gwamnan Imo na NNPP a Abuja, bayan da ya karbi takardar sheda a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar a NNPP.