Daga: Rabilu Sanusi Bena
Tawagar kwallon kafa ta kasar Sifen ta samu nasarar lashe kofin kasashen Turai bayan nasarar da ta samu akan abokiyar karawarta Kurotiya
Sifen wadda ta lashe kofi a karon farko cikin shekaru 11 ta buga mintuna 90 ba tare da zura kwallo a ragar Kurotiya ba abinda yasa Alkalin wasa ya bushe wasan kuma ya kara mintuna 30 domin cigaba da fafatawa.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Kano Ya Biya Bashin da NECO Take Bin Jihar
Daga karshe dai aka tashi wasan babu ci wanda yasa aka tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga
Dan wasan Real Madrid Dani Carvajal ne ya zura kwallo ta karshe kuma wadda ta zama dalilin lashe kofin da kasarsa tayi.
Dan wasan tsakiyar Manchester City Rodri wanda aka bawa kyautar mafi kokari a wasan ya bayyana lashe kofin a matsayin wani sabon babi da kasarsa ta bude a harkar kwallon kafa ganin cewar akwai matasan yan wasa masu tasowa.
‘Yan wasan sun hada da Ansu Fati,Yeremy Pino da kuma Pablo Gavi Dake taka leda a Fc Barcelona
Modric yayi fatan ya ci wa kasarsa Kofi na Farko a tarihinta a matsayin sa na kyaftin din tawagar Kasar ta Kudancin Turai amma hakan Bai yiwu ba ga dan Shekara 34 da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d’or a shekarar 2018
A wani labarin kuma,Iyakokin Arewa Yanzu Sun Koma Matattarar Fataucin Bil-Adama – NAPTIP
Hukumar hana fataucin mutane ta kasa ta koka kan yadda masu safarar mutane ke karuwa ta hanyar kan iyakokin arewa.
Darakta-Janar ta Hukumar NAPTIP, Farfesa Fatima Waziri-Azi, ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da jaridar PUNCH a wajen taron hadin gwiwa da aka kammala kwanan nan kan wata yarjejeniya da Najeriya da Gambia suka sanya wa hannu, wanda aka gudanar a Abuja.