Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kasafin kudin jihar na Shekara ta 2022 dake tafe a gaban zauren Majalisar dokoki ta jihar a yau Alhamis.
Yawan kudin da kasafin ya kunsa ya kai Naira Biliyan 196, wanda kuma an samu raguwa idan aka kwatanta shi dana shekarar 2021, da yawan kudin ya kai sama da Naira biliyan 197.
To sai dai Gwamna Ganduje ya bayyanawa Majalisar cewa daga cikin kudin kasafin za a ware Naira biliyan 107 domin aiwatar da manyan ayyukan wanda kuma kudin ya kunshi kaso 55 na kasafin.
Kazalika bangaren Ilimi, Ayyukan more rayuwa, lafiya, su kuma zasu dauki kaso mafi tsoka daga cikin kasafin.