- Gwamnan Katsina Dikko Radda ya rattaba hannu kan karin kasafin kudi sama da biliyan 300.6 na shekarar 2023
- Daukar matakin ya nuna aniyar gwamnati na ba da fifiko ga jin dadin ‘yan jiha da samar da yanayi mai aminci da wadata ga dukkan mazauna jihar
- Karin kasafin kudin shi ne domin yaki da rashin tsaro, rage radadin talauci, da bayar da tallafi ga marasa galihu a fadin jihar
Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya rattaba hannu kan karin kasafin kudi sama da biliyan 300.6 na shekarar 2023.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed,shi ne wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN: Sojoji sun ceto mutane 18 da aka yi garkuwa da su a jihohin Arewa
Ya ce za a tura karin kasafin kudin ne domin yaki da rashin tsaro, rage radadin talauci, da bayar da tallafi ga marasa galihu a fadin jihar.
Ya ce kakakin majalisar dokokin jihar, Nasir Yahya-Daura ne ya mika wa gwamnan karin kasafin kudin a ranar Juma’ar da ta gabata.
“Wannan matakin ya nuna aniyar gwamnati na ba da fifiko ga jin dadin ‘yan jiharta da samar da yanayi mai aminci da wadata ga dukkan mazauna jihar,” in ji Mohammed.
Da yake jawabi a wurin rattaba hannun, Radda ya bayyana fatan cewa karin kasafin zai taimaka wajen ciyar da jihar gaba da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga mazauna yankin.
Ya yabawa ‘yan majalisar bisa namijin kokarin da suka yi wajen tsara kasafin, ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa.
Hakazalika gwamnan, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin kasaftawa da amfani da albarkatun kasa domin ci gaban jihar.
DAILY POST ta rahoto cewa Radda ya bukaci majalisar ta amince da karin kasafin kudin domin kara kasafin kudin shekarar 2023 na Naira biliyan 289.6 wanda tsohon gwamnan jihar Aminu Masari ya sanya wa hannu a watan Disambar shekarar 2022.
A wani labarin kuma, Yaki: Rasha ta Kai Mummunan Hari a Babban Birnin Ukraine, Kyiv
Dakarun Rasha sun kai hari a Kyiv babban birnin Ukraine da jirage marasa matuka a safiyar Lahadi.
A cewar CNN, shaidu sun ji karar fashewar abubuwa akalla biyar amma har yanzu ba a tantance girman harin ba.