Gwamnan Kogi ya naɗa Sabbin Manyan Sakatarori guda 10
Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello ya amince da naɗa Sabbin Manyan Sakatarori guda 10 a Ma’aikatun Gwamnati.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugabar Ma’aikata Mrs Hannah Odiyo ta sanyawa hannu, inda tace Sabbin Manyan Sakatarori da aka naɗa, zasu zama madadin waɗanda suka ajiye aikin Gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Wannan Babban Tsokana Ne”—- Koriya Ta Kudu Ta Koka, Bayan Koriya Ta Arewa Ta Gwada Makamai Masu Linzami A Yau
Sanarwar ta bayyana cewar an yi naɗin ne a bisa cancanta,domin inganta aikin Gwamnati a Jahar.
Shugabar Ma’aikatan tayi kira ga Sabbin Manyan Sakatarori dasu zama masu halin dattaku, gami da zama masu biyayya ga Gwamnati a wajen gudanar da ayyukan su.
Odiyo ta taya Sabbin Manyan Sakatarori murna da naɗa su da akayi, gami da bada tabbacin Gwamnati na inganta jindaɗin Ma’aikatan Jahar.
Ta yabawa Gwamnan daya amince da naɗa su, da kuma irin ayyukan cigaba wajen inganta jindaɗin Ma’aikata domin ƙarfafa ƙwazon su.
Comments 1