By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda shida a ma’aikatun gwamnati daban daban.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Mista Abari Aboki ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Adamawa Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Kyandar Biri Na Kamuwar Mutane 5, Tare Da Zargin Wasu 57
Aboki ya taya sabbin sakatarorin dindindin murna bisa nadin da aka yi musu.
Sunayen Sabbin Sakatarorin sun hada da Chammang Atinuke, Ada Maikefi, Isa Muhammad Eyah, Hussain Usman, David Galadima da Abdulkareem Ibn Bala.
Ya ce nadin nasu ya biyo bayan ritayar da wasu sakatarorin dindindin na ma’aikatun jihar daban daban suka yi
Shugaban ma’aikatan ya ce za a sanar da jama’a ranar da za a rantsar da su nan gaba kadan.(NAN)
A wani labarin kuma Jihar Adamawa ta ce ta tabbatar da mutane 5 wadanda suka kamu da cutar kyandar biri, kuma tana duba wasu mutane 57 da ake zargin sun kamu da cutar.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ta ce ta samu dakunan gwaje-gwajen da aka tabbatar da mutane biyar sun kamu da cutar tun daga ranar 12 ga watan Yuni.
Daraktar Kiwon Lafiyar Jama’a, Dr. Celine La’ori, ta fada a wata hira da manema labarai cewa an samu bullar cutar ta farko a watan Afrilu a babban birnin jihar, Yola.
Ta bayyana cewa, har ya zuwa yau, yaduwar cutar ta barke a kananan hukumomin biyu na Yola ta Arewa da Yola ta Kudu.
La’ori ta ba da tabbacin cewa, domin dakile yaduwar cutar, an kafa cibiyar bayar da agajin gaggawa.
“Wannan ne karon farko da aka samu bullar cutar a jihar, don haka abokan aikinmu ne suka horar da ma’aikata. Mun kuma fara aikin wayar da kan jama’a zuwa yankunan da abin ya shafa,” inji ta.
Ta yi gargadin cewa cutar kyandar biri na da saurin yaduwa kuma ya kamata a ware masu kamuwa da cutar tare da kula da tsaftar su.
La’ori ta ce alamomin kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, tare da rashi kuzari kamar murar tsuntsaye.
“Lokacin da kuke da irin wannan rashi kuzari, ku garzaya cibiyar aikin lafiya ta gaggawa don gano ainihin cutar data ke damunku ,” in ji ta.
Kazalika Laori ta koka da karancin ilimin da mutane suke dashi game da kwayar cutar tare da yin kira da a wayar da kan jama’a yadda ya kamata.
Comments 1