- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya sanar da ranar da zai kaddamar da rabon kayan tallafin ga sama da gidaje 200,000
- Kananan hukumomin sun ba da gudummawar Naira biliyan 2.63 yayin da gwamnatin jihar ta saka Naira biliyan 5.99 don bada tallafin
- Gwamnatin ta ce za a yi rabon ne a rukuni daban-daban da nufin rage radadin da mazauna yankin ke fama da su sakamakon cire tallafin man fetur
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a ranar Laraba zai kaddamar da rabon kayan tallafin ga sama da gidaje 200,000 a fadin jihar.
Taron ranar laraba wanda za’ayi a garin Oyo zai biyo baya ne inda za’a raba shi zuwa sauran shiyyoyin siyasa daga ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN: Kano: Shugaban Jam’iyyar NNPP Ya Magantu Kan Dakatar da Kwankwaso
Kayayyakin da za a raba sun hada da buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 10, man garri kilo 5, buhun wake mai nauyin 5kg, buhun elubo mai nauyin 5kg da kuma lita 1 man abinci.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Mista Dotun Oyelade, wanda ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, ya ce an ware naira biliyan 8.63 domin raba tallafin rage radadi.
Oyelade ya ce kananan hukumomin sun ba da gudummawar Naira biliyan 2.63 yayin da gwamnatin jihar ta saka Naira biliyan 5.99.
Oyelade ya ce za a yi rabon ne a rukuni daban-daban da nufin rage radadin da mazauna yankin ke fama da su sakamakon cire tallafin man fetur.
“Idan ka dauka cewa kowane iyali yana da kusan mambobi 6, muna magana ne game da mutane sama da miliyan 1 da farkon shirin ya shafa,” in ji Oyelade.
Da yake karin haske, kwamishinan kasafin kudi na jihar, Farfesa Musbau Babatunde, ya ce gwamnati ta ware Naira miliyan 149.1 ga karamin kwamitin sufuri.
Ya ce kasafin kudin ya hada da kayan aiki, alamar motocin bas, ma’aikata, da kuma kudin man dizal.
Ya kara da cewa, mabukata 100,000 na al’umma kuma gwamnatin jihar za ta kula da su.
Kwamishinan ya kara da cewa jami’an tsaro da suka hada da Amotekun, Sojojin Najeriya, ‘yan sanda, da Civil Defence, wadanda su ne sahun farko na tsaro a jihar, za su ci gajiyar tallafin.
Har ila yau, ma’aikatan gwamnati da ke cikin ƙananan matakai na ma’aikatan gwamnati za su kasance masu cin gajiyar wannan karimcin.
Babatunde ya tabbatar wa mazauna yankin yadda ya kamata wajen rabon kayayyakin, yana mai cewa gwamnatin jihar Oyo ta sanya tsarin sa ido da tantancewa.
Dangane da batun samar da abinci, wanda zai baiwa manoma da kanana da matsakaitan masana’antu, gwamnatin jihar Oyo, ya ce gwamnati ta ware Naira miliyan 1.701 yayin da rancen da za a bayar ga SMEs zai ci Naira miliyan 510.
A bangaren kiwon lafiya, Kwamishinan ya ce an ware Naira biliyan 1 domin kula da Inshorar lafiya na ‘yan fansho 50,000, kan Naira 4,000 kowanne.
A wani labarin kuma,Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Kori Manyan Jami’an NDDC, Ya Sanar da Sunayen Sabbi
Shugaba Bola Tinubu ya rusa hukumar gudanarwar raya yankin Neja Delta (NDDC) karkashin jagorancin Lauretta Onochie
A watan Nuwambar shekarar 2022 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Onochie a yayin da hakan ya haifar da cece-kuce
Canje-canjen ya kuma shafi wasu dake jagorancin hukumar ta NDDC
Kasa da shekara guda da nada ta, shugaba Bola Tinubu ya rusa hukumar gudanarwar raya yankin Neja Delta (NDDC) karkashin jagorancin Lauretta Onochie.
A madadinta, ya nada sabon shugaban hukumar karkashin jagorancin Chiedu Ebie daga jihar Delta a matsayin shugaba.