Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya mayar da martani kan rahoton dakatarwar da aka yi wa jagoran jam’iyyar na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso.
Dungurawa ya shaidawa DAILY POST a ranar Talata cewa, ba a dakatar da Kwankwaso daga jam’iyyar ba, ba wani abu ba, “a yanzu haka yana halartar babban taron NEC na jam’iyyar a Abuja.”
KARANTA WANNAN: Jam’iyar NNPP Ta Dakatar Da Kwankwaso Daga Shiga Harkokin Jam’iyar Akan Zargin Yi Mata Zagon Kasa
Ya dage cewa Kwankwaso na da kima a cikin jam’iyyar NNPP kuma an amince da shi a matsayin halaltaccen shugaba, inda ya ce zargin dakatar da shi karya ne da kuma bata masa suna.
Ya ce, “Kwankwaso ne shugaban jam’iyyar kuma wani ya fito da labarin karya na dakatarwar da aka yi masa, tamkar jan sunayensa ne da kwarjinin mutuncinsa ga laka.
“A yanzu haka ina Abuja inda shugabannin jam’iyyar ke gudanar da taro, babu wani abu makamancin haka,” in ji shi.
A wani labarin kuma,Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Kori Manyan Jami’an NDDC, Ya Sanar da Sunayen Sabbi
Shugaba Bola Tinubu ya rusa hukumar gudanarwar raya yankin Neja Delta (NDDC) karkashin jagorancin Lauretta Onochie
A watan Nuwambar shekarar 2022 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Onochie a yayin da hakan ya haifar da cece-kuce
Canje-canjen ya kuma shafi wasu dake jagorancin hukumar ta NDDC
Kasa da shekara guda da nada ta, shugaba Bola Tinubu ya rusa hukumar gudanarwar raya yankin Neja Delta (NDDC) karkashin jagorancin Lauretta Onochie.
A madadinta, ya nada sabon shugaban hukumar karkashin jagorancin Chiedu Ebie daga jihar Delta a matsayin shugaba.