Gwamnan Sokoto ya karbi mutane 66 da sojojin Najeriya suka ƙwato
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya karbi bakuncin mutane sittin da shida wadanda aka yi garkuwa da su da sojoji hadin gwiwa na rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma ‘Operation Hadarin Daji’, OPHD, na Sojojin Najeriya suka ceto.
A lokacin da yake karbar wadanda abin ya shafa, gwamnan ya yabawa dakarun sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Banida Masaniya Akan Abinda Ake Zargina Da Aikatawa-Sadiya Umar Faruk
“A yau, mun sake shaida wani muhimmin abu, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su daga kauyuka da al’ummomi daban-daban a karamar hukumar Isah ta jihar,” inji shi.
Aliyu ya bayyana cewa, bisa bayanan da aka tattara, an samu nasarar ceto mutane 52 a ranar Alhamis, 22 ga Disamba, 2023, yayin da aka ceto 14 da suka mutu a ranar Asabar, wanda ya kai 66.
Ya kara da cewa a kwanakin baya ne gwamnatin sa ta bayar da gudumawar motoci tamanin (80) ga dukkanin hukumomin tsaro domin bunkasa ayyukansu a fadin jihar.
Gwamna Aliyu ya bukaci al’ummar jihar da su rika bayar da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro a kodayaushe domin tsaron jihar baki daya.
Tun da farko, yayin da yake gabatar da wadanda aka ceto ga gwamnan, kwamandan Garrison Division 8 na sojojin Najeriya, Birgediya Janar Alex Tawasimi, ya ce an ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda.
Wadanda aka ceto sun hada da maza 14, mata 32, da kuma kananan yara 6 da aka yi musu duban lafiya tare da bayyana ra’ayoyinsu, kuma yanzu haka an mika su ga gwamnatin jihar domin sada su da iyalansu.
Kwamandan rundunar ya yabawa gwamnan bisa goyon bayan da yake bayarwa wajen samun nasarar ayyukansu, yana mai bada tabbacin cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Sokoto da kewaye.
A wani labarin kuma:Banida Masaniya Akan Abinda Ake Zargina Da Aikatawa-Sadiya Umar Faruk
Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce ta kama wasu mutane 8 da ake zargi da hannu a kisan wani basaraken gargajiya na yankin Adani mai cin gashin kansa da ke unguwar Uzo Uwani, Igwe Ezugwu Patrick.
An rahoto cewa an kashe Igwe Patrick ne a kauyensa, Akutara ranar Lahadi.