Yan sanda sun cika hannu da mutanen da suka hallaka Sarkin Enugu
Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce ta kama wasu mutane 8 da ake zargi da hannu a kisan wani basaraken gargajiya na yankin Adani mai cin gashin kansa da ke unguwar Uzo Uwani, Igwe Ezugwu Patrick.
An rahoto cewa an kashe Igwe Patrick ne a kauyensa, Akutara ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zamfara ta ware biliyan 1.95 ga fadar sarakunan gargajiya
A wata ziyara da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kanayo Uzuegbu ya kai wa al’umma a ranar Litinin, ya bayyana cewa an kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a kisan.
Uzuegbu ya ce ya je unguwar tare da tawagarsa domin tantance halin da ake ciki domin daukar kwararan matakai na ‘yan sanda.
Ya ci gaba da cewa duka masu shirya da kuma masu aiwatar da wannan aika-aikar za a kama su ne domin fuskantar fushin doka.
Shugaban ‘yan sandan ya ce, “Gwamnan jihar Enugu ya ce ya kamata in koma wannan karamar hukumar sannan in tabbatar da cewa an kama duk wadanda suka aikata wannan aika-aika kamar yadda jihar ba ta da hurumin aikata laifuka.
“Nan da nan labari ya iso gare ni, na aika da mazana daga sashin binciken manyan laifuka da kuma ’yan sandan yankin, karkashin jagorancin kwamandan yankin, domin su kai ziyara nan, su tabbatar an kama duk wadanda ke da hannu a ciki, domin babu wani abu makamancin haka da zai faru ba tare da wani mummunan sakamako ba.
A wani labarin kuma:Xmas: Kungiyar CAN Ta Bukaci Ƴan Nijeriya Kan Zaman Lafiya Da Sulhu
Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta bukaci ƴan Najeriya da su yi amfani da bukukuwan Kirsimeti domin zama masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kuma samar da sulhu na gaskiya.
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya yi wannan kiran a ranar Litinin a sakonsa na Kirsimeti a madadin Kiristocin Najeriya.