Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni ya yaba wa Sojojin Najeriya kan fatattakar ‘yan Boko Haram da suka yi a Gujba a ranar Asabar. Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ‘Yan Jarida da Harkokin Watsa Labarai na gwamna, Mohammed Mamman ya sanya wa hannu a safiyar ranar Lahadi.
Jaridar Walkiya ta samu labarin cewa wasu gungun maharan sun yi wa ayarin motoci kwanton-bauna a hanyar Damaturu-Gujba-Buni Yadi da yammacin ranar Asabar lamarin da ya kai ga kone wasu gidaje da ba a san adadinsu ba, duk da cewa hukumomin tsaro sun yi shiru da bayanan.
Mamman ya ce jajircewar da jami’an tsaro suka yi wajen fatattakar masu tayar da kayar bayan ya samu nasarori kuma zai sauya labaran da ake bayarwa wajen yaki da tayar da kayar baya da kyakkyawan sakamako. “Juriya da jaruntakar sojoji abin a yaba ne kwarai da gaske kuma dole ne a yaba musu don kara musu kwarin gwiwa”.
Gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu yabawa da marawa jami’an tsaro baya ga yawan kalubalen tsaro a fadin kasar. Gwamna Buni ya ba da tabbacin goyon baya ga gwamnati da mutanen jihar Yobe ga tsaro, wannan yakar juna ce kuma dukkanmu muna da hannu”.
Gwamnati za ta ci gaba da ba mu goyon bayan da ya dace domin mu samu zaman lafiya a jihar”. Gwamnan ya yi kira ga mutane da su rika samar da bayanai masu amfani a kan lokaci game da motsin da ba su dace ba a cikin al’ummominsu ga hukumomin gwamnati da jami’an tsaro don daukar matakan da suka dace.
Gwamna Buni ya yi nadamar asarar rayukan da aka samu kuma ya yi fatan wadanda suka jikkata su samu lafiya cikin gaggawa. Ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta bayar da tallafi na gaggawa ga wadanda abin ya shafa. Gwamna Buni ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta ba da taimakon da ake bukata ga mutane tare da ba wa gwamnati cikakken bayanin irin barnar da aka yi a harin don daukar matakin da ya dace.