- Gwamnatin Delta karkashin jagorancin gwamna Sheriff Oborevwori ta bai wa wani dan kwangila da ke gudanar da aikin gina wasu ayyuka wa’adin sa’oi 48 don yin bayani dalla-dalla
- Ka fin daukar wannan matakin gwamnati ta tuntubi dan kwangilar, don cigaba da aikin amma ya yi watsi da umarnin
- Muddin ya kasa tabuka abin azo agani za’a dauki matakin daya dace
Gwamnatin jihar Delta ta bai wa dan kwangilar da ke gudanar da aikin ginin a Lander Brothers Anchorage, Asaba wa’adin sa’oi 48 da ya bayyana dalilin da ya sa ba za a soke kwangilar ba, Daily Post ta rawaito.
Kwamishinan al’adu da yawon bude ido, Darlington ljeh, wanda ya ba da wannan umarni a ranar Talata, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta sayar ba, kuma ba ta da niyyar siyar da Lander Brothers’ Anchorage ga mutane masu zaman kansu.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokoki Ta Amince da Bukatar Gwamna Makinde Ta Ciyo Bashin Biliyan N50bn
Ijeh ya bayyana cewa an bayar da kwangilar ne ga Messrs Jabi Boat Club Abuja a ranar 1 ga watan Disambar shekarar 2020, kuma a yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin jihar, kamfanin zai gina, aiki da kuma canja wurin a cikin wani ƙayyadadden lokaci, tare da tsamanin fara aiki da ginin a 2023.
Ya kuma jaddada cewa duk wani dan kwangilar da ya ke a wurin shi ne rusa ginin da ya kasance wurin yawon bude ido da kuma samar da kudaden shiga ga jihar da kuma matasan al’ummar da ke da kananan sana’o’i inda Lander Brothers’ Anchorage yake a Asaba.
Ijeh ya kara da cewa an tuntubi dan kwangilar ne a cikin watan Agusta, 2023, inda ya bukaci kamfanin ya koma wurin da kuma sake gina ginin da aka ruguje, amma Messrs Jabi Boat Club Abuja ya yi watsi da umarnin, kuma har ya zuwa yau, babu ko daya daga cikin kamfanin ganin a wurin.
Ya kuma kara da cewa an bayar da kwangilar ne ga kungiyar Messrs Jabi Boat Club da ke Abuja a rana guda tare da wurin shakatawa na Maryam Babangida Leisure Park da Film Village, inda ya ce an gina wurin, an mika shi ga gwamnatin jihar, daga bisani aka ba da izinin yin amfani da shi. ta Deltans.
A wani labarin kuma,Kano: Dan Ganduje Ya Yi Rashin Nasara A Kutun Sauraren Kararrakin Zabe
Kotun sauraren kararrakin zabe a Kano ta yi watsi da karar da Abba Ganduje, dan tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya shigar
Kotun ta umarce shi da ya biya wadanda ake kara Naira 200,000 kowannensu
Alkalan kotun sun yi watsi da karar saboda rashin cancantar ta
Kotun sauraren kararrakin zabe a Kano ta yi watsi da karar da Abba Ganduje, dan tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya shigar kan rashin cancantar ta.
Kotun ta umarce shi da ya biya kowannen su Naira 200,000 ga wadanda ake kara Tijjani Abdulkadir Jobe, jam’iyyar NNPP, da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC.