Gwamnatin jihar Osun ta dakatar da sabon tsarin biyan kudin makaranta da majalisar gudanarwar kwalejin fasaha ta jihar Osun, Iree ta amince da shi.
Hakan ya zo ne kamar yadda hukumar Kwalejin ta sanar da shirin ta na bin umarnin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NEMA Ta Kwaso ‘Yan Najeriya 191 Da Suka Makale Daga Kasar Indiya
Sabon tsarin biyan kudin makaranta tun asali an yi shi ne ga sabbin daliban da suka samu shiga a kowane mataki a makarantar.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun A.O. Okediya, mai kula da sha’anin kudi na cibiyar da ke sanar da shirye-shiryen gudanar da kwalejin ta hanyar bin umarnin ya bayyana cewa, umarnin dakatarwar ya shafi daliban ND I da HND I ne kawai.
A cewarsa: “Bisa umarnin gwamnatin jihar, an dakatar da sabon tsarin biyan kudin da majalisar gudanarwar cibiyar ta takwas ta amince da sabbin daliban da suka samu gurbin karatu na shekarar 2022/2023, har sai an samu karin umarni daga gwamnatin jihar.
“Don Allah a lura cewa wannan umarnin ya shafi ɗaliban ND I da HND I ne kawai, ana sa ran sauran nau’ikan ɗalibai za su ci gaba da biyan rajista kamar yadda ake sa rai.”
Gwamnan jihar, Ademola Adeleke a ranar Litinin din da ta gabata yayin wani rangadin da ya kai wasu makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a jihar ya koka da rashin kyawun kayan aiki.
Adeleke ya kuma yi alkawarin a cikin kwanaki dari 100 a kan karagar mulki, zai juyo da fannin ilimi daidai da alkawuran yakin neman zabensa da kuma tsare-tsare guda biyar na ayyukan jihar.
A wani labarin kuma, Kayyade Cirar Kudi: Masu Sana’ar POS Suna Son Dakatar Da Manufar CBN
Kungiyar masu sana’ar cirar kudi ta na’ura da wakilan bankuna a Najeriya, wadanda aka fi sani da masu POS, sun yi kira ga babban bankin Kasa (CBN) da ya dakatar da manufofinsa na takaita cirar da kudade.
Babban bankin, a karkashin sabuwar manufar cire kudi, ya takaita adadin kudaden da mutane da kungiyoyi da kamfanoni ke karba a duk mako zuwa Naira 100,000 da Naira 500,000.
Babban bankin ya kuma kayyade masu POS zuwa Naira 20,000 a kowace rana. Ana ayya manufofin zata fara aiki a ranar 9 ga Janairun 2023.