Gwamnatin Bauchi Ta Bada Tallafin Karin Kuɗin Aikin Hajji Da Kashi 50%
Domin rage radadin ƙarin kudaden aikin hajjin da aka kara wa maniyyatan jihar, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya amince da bayar da tallafi kashi 50 cikin 100, wanda ya kai Naira 950,000, na aikin hajjin 2024 ga kowane maniyyacin jihar.
DAILY POST ta ruwaito cewa Hukumar Alhazai ta kasa ta kara kudin jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya da Naira N1,918,032.91.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ƴan sanda sun damƙe ƴan ta’adda 15 a Gombe
Dangane da wannan ci gaban, gwamnatin jihar ta ce za ta biya tallafin Naira 959,000 ga duka mahajjata 1,652 daga jihar, wanda ya kai Naira biliyan 2.5.
Mukhtar Gidado, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A wani muhimmin mataki da aka dauka na saukaka ayyukan addini da kuma inganta rayuwar al’ummarta, mai girma Gwamnan Jihar Bauchi ya amince da bayar da tallafin kudin aikin Hajji ga dukkan maniyyatan jihar.
“Wannan mataki mai cike da tarihi ya biyo bayan sanarwar da Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta yi a baya-bayan nan game da daidaita farashin Hajjin 2024, inda a yanzu ake bukatar maniyyata su biya karin kudi har miliyan daya da dubu dari tara da goma sha takwas da hamsin (N1,918,050).
“A bisa abubuwan da suka gabata, gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed, ta bayar da tallafin kudi har naira dubu dari tara da hamsin da tara, da naira ashirin da biyar (N959,025.00) wanda ya kai kashi 50% na kudin. Karin kudin da ke sama ga kowane mahajjata 2,290 daga jihar Bauchi.”
“Saboda abubuwan da suka faru a sama, gwamnan ya kuma amince da a gaggauta sakin zunzurutun kudi biliyan biyu da dubu dari daya da casa’in da shida, da naira dari da goma (N2,196,110) kawai domin biyan kudin tallafin.
“Wannan ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba ya nuna aniyar gwamnati na ganin cewa Musulmin jihar Bauchi sun samu damar sauke nauyin da aka dora musu na aikin Hajji a Makka, daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.
A wani labarin kuma:Yanzu-Yanzu: Daga Aljihunsa, Shugaba Tinubu ya ɗauki nauyin saka AC a babban masallacin Juma’a na ƙasa
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe karkashin jagorancin CP Hayatu Usman, ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a ci gaba da yaki da miyagun laifuka a jihar.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Mahid Muazu Abubakar, an kama mutanen ne a kokarin da rundunar take yi na yaki da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron mazauna yankin da kuma masu ziyara.