Yadda wani matashi ɗan jihar Bauchi ya caka wa wani abokinsa wuƙa
Wani bala’i ya afku a karamar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi yayin da Adamu Isa dan shekara 15, dan wani jami’in dan sanda mai ritaya, ya caka ma abokinsa wuƙa Abubakar Isa.
An ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris bayan wata zazzafar cece-kuce tsakanin abokanan.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-Yanzu: Daga Aljihunsa, Shugaba Tinubu ya ɗauki nauyin saka AC a babban masallacin Juma’a na ƙasa
Jaridar DAILY POST ta ruwaito wannan lamari na baya-bayan nan yana zuwa ne kwanaki biyu kadan bayan wani yaro dan shekara 16 ya daba wa wani matashi mai shekaru 25 wuka har lahira a wani gari na jihar Bauchi.
DAILY POST ta samu labarin cewa wanda ake zargin ya daba wa marigayin wuka a wuyansa kusa da makogwaro, lamarin da ya kai ga mutuwarsa nan take, tun kafin a kai shi asibiti.
Sai dai kuma har yanzu ana kan zayyana abin da ya kai ga fadan.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakili, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’ar da ta gabata, ya shaida wa DAILY POST cewa, a ranar ne rundunar ‘yan sandan Ningi ta samu kiran gaggawa daga DSP Kasuwa Isa mai ritaya, wanda ke zaune a bayan ofishin INEC da ke Ningi.
A cewar Wakil, Isa ya ruwaito cewa dansa mai suna Adamu Isa mai shekaru 15, wanda ke zaune a bayan ofishin NEPA da ke Ningi ya daba ma abokinsa wuƙa a wuyansa.
“Da samun korafin, DPO na sashin Ningi ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Ningi, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa,” inji shi.
Wakil ya kara da cewa, an kama wanda ake zargin Abubakar Isa, kuma yana hannun ‘yan sanda har sai an gudanar da bincike kan lamarin.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Bauchi Ta Bada Tallafin Karin Kuɗin Aikin Hajji Da Kashi 50%
Domin rage radadin ƙarin kudaden aikin hajjin da aka kara wa maniyyatan jihar, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya amince da bayar da tallafi kashi 50 cikin 100, wanda ya kai Naira 950,000, na aikin hajjin 2024 ga kowane maniyyacin jihar.
DAILY POST ta ruwaito cewa Hukumar Alhazai ta kasa ta kara kudin jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya da Naira N1,918,032.91.