Gwamnatin Borno zata raba magungunan sama da Naira Miliyan 800 ga manyan Asibitocin Jihar
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ƙaddamar da rabon magungunan mata masu juna biyu kyauta na sama da Naira miliyan 800 ga manyan asibitoci biyar na Jihar domin kula da lafiyar mata masu juna biyu.
An gudanar da rabon kayayyakin ne a ranar Alhamis a babban ɗakin ajiye magani na jihar Borno dake Maiduguri.
Asibitocin da suka amfana sun hada da asibitin kwararru na Jihar da ke Maiduguri, da Mohammed Shuwa Memorial Hospital, da Umaru Shehu Ultra Modern Hospital, da Mariam Abatcha Children Hospital da Molai General Hospital.
Baya ga magungunan, kowacce asibiti za ta samu tallafin Naira miliyan 5 yayin da Asibitin kwararru wanda shi ne mafi girma a Jihar zai samu ƙarin Naira miliyan 5 wato asibitin za ta samu Naira Miliyan 10 kenan.
KARANTA NAN:“Babu Amfanin ɗaukaka ƙara, Ku zo a haɗa kai domin gyara Najeriya” – Gwamnan Kogi ga Atiku da Obi
Zulum a Jawabinsa ya ce, “A yau mun zo ne domin kaddamar da rabon magungunan mata masu juna biyu da sauran kayayyakin da ake bukata a ɓangaren mata ga wasu asibitocin mu don tallafa ma marasa galihu a jihar, Wannan zai rage mace-macen mata masu juna biyu da kuma kara yawan kula da yara a Jihar”.
Gwamnan ya kuma raba kayan aikin tiyata da wasu kayayyaki na dakin gwaje-gwaje domin inganta ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar jihar Borno.
Ya kuma bukaci hukumar kula da asibitocin da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu inda ya ce “Ina so in yi kira ga ɗaukacin ku da ke aiki a fannin kiwon lafiya da ku kara hakuri da kuma kwazo domin Gwamnati ta kawo muku agajin da za mu magance,
al’amurran da suka shafi aikin ku, kamar alawus da sauran su.
Sai dai Zulum ya yi gargadin cewa Gwamnatin sa ba za ta amince da lalaci da kuma rasbin gogewar aiki ba.
“Mun saka kuɗaɗe sosai a fannin kiwon lafiya a cikin shekaru hudu da suka gabata amma abin takaici ba mu ganin ana samun cigaban da ake buƙata”, inji shi.
A wannan karon ba za mu lamunci lallashin ma’aikata ba, babba ko ƙarami, Dole ne mu tsaftace tsarin domin ba za mu yi wasa da tsarin kiwon lafiyarmu ba, ”in ji shi.
Da yake jawabi tun da farko kwamishinan lafiya na Jihar Farfesa Baba Mallam Gana da babban daraktan kula da lafiya Farfesa Bukar Kullima a Jawabansu daban-daban sun bayyana godiya ga Gwamnan bisa jajircewa da goyon bayansa ga fannin kiwon lafiya a Jihar Borno.