“Zan garzaya Kotun ƙoli domin neman adalci” – Peter Obi
Ɗan takarar Jam’iyyar Labour a zaɓen Shugaban ƙasar Najeriya da aka gudanar a shekarar 2023, Peter Obi, ya nemi lauyoyinsa da su ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun sauraren ƙorafe-ƙorafen zaɓen Shugaban ƙasa ta yanke inda ta jaddada nasarar Bola Ahmad Tinubu a zaɓen.
Da yake zantawa da manema labarai a birnin Onitsha na Jihar Anambra, Mr. Peter Obi ya ce suna mutunta hukuncin kotun amma za su matsa gaba domin neman adalci.
Obi yace “A matsayinmu na masu ƙorafi, muna mutunta hukuncin kotun, amma ba mu yarda da hanyoyin da ta bi ba wajen yanke hukuncin, don haka za mu garzaya zuwa kotu ta gaba.
Ya ƙara da cewar, “a matsayina na ɗan takara da kuma jam’iyyata ta Labour Party LP za mu ƙalubalanci wannan hukunci ta hanyar ɗaukaka ƙara, kamar yadda kundin tsarin mulki na Najeriya ya bayar da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN:“Babu Amfanin ɗaukaka ƙara, Ku zo a haɗa kai domin gyara Najeriya” – Gwamnan Kogi ga Atiku da Obi
“Tuni tawagarmu ta lauyoyi ta samu umarnin ɗaukaka ƙarar. Ba zan taɓa sarewa ba wajen neman adalci, ba don kaina ba sai don dubban magoya bayanmu a faɗin ƙasa da wajenta.” Inji shi.
A jiya Laraba ne dai alƙalan kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ƙarƙashin Mai Shari’a Haruna Tsamani suka yi watsi da buƙatar da Obi da Atiku na jam’iyyar PDP suka gabatar, sannan Kotun ta jaddada cewa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen na watan Fabrairu.
A wani labarin kuma:Gwamantin Gombe ta rufe Gidajen Gala 5 a Jihar
Gwamantin Gombe ta rufe Gidajen Gala 5 a Jihar
Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta rufe wasu gidajen gala guda biyar da ke yankunan Tunfure da BCGA a cikin kwaryar birnin Jihar.
Wannan wani kokari ne da kwamitin ya yi na aiwatar da umarnin da Gwamnan Jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayar na rufe dukkanin gidajen gala da ke faɗin Jihar tare da hana su gudanar da ayyukansu sakamakon korafe-korafen jama’a game da ayyukansu.