Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar ya ce matsalar fashin daji da fadar fulani da makiyaya ya samo asali tun chan baya ba wai kan mulkin Shugaban KAsa Muhammadu Buhari aka fara ba, inda a cewar shi sakacin gwamnatocin baya ne ya kai ga ta’azzarar lamarin kawo haka.
Da yake magana cikin wani shirin siyasa na Tashar Talabijin na Channels mai suna Politics Today” wato Siyasar Mu a Yau, gwamna Badaru ya ce Shugaba Buhari ya gaji al’amarin yayin hawan shi karagar mulki a shekarar 2015 kuma haka aka ci gaba da tafiya har kawo yanzu.
Gwamnan ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta aiki tukuru wajen ganin an shawo kan tsaro inda ya ce matsalar tashin Boma-bomai ya ragu matuka a kasar nan ba kamar chan baya ba.
“Idan muka sanya batun a ma’auni, ba wai an fara wadannan matsalolin fashin dajin da kuma na sace sacen jama’a a mulkin Buhari ba ne, shi ma dai gado ya yi” Cewar Badaru.
Ya kara da cewa “Gabannin zuwan Buhari Karagar Mulki, matsalar bama-bamai ya zama tamkar ruwan dare a Najeriya, an yi Jihar Kano, an samu kuma a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja. amma daga hawan shi mulki al’amarin ya tsagaita. An kuma yi nasarar karbe dukkanin kananan hukumomi dake hannun kungiyar Boko Haram.