Gwamnatin jihar Imo ta nesanta kanta kan tsare tsohon mataimakin gwamnan jihar Gerald Irona kamar yadda Punch ta rawaito.
A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an rundunar ‘yan sandan jihar suka kama Irona a garin Owerri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kano: Ganduje Ya Nada Sabuwar Babbar Alkalin Riko Ta Jihar
Sa’o’i kadan bayan kama shi, kakakin tsohon mataimakin gwamnan da kuma jam’iyyar PDP reshen jihar a wata sanarwa daban-daban sun yi ikirarin cewa gwamnatin jihar ce ta shirya kama shi.
Sai dai gwamnatin jihar ta musanta wannan ikirarin, inda ta ce gwamnan jihar, Hope Uzodimma, ba ya tsoma baki cikin harkokin ‘yan sanda.
Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa, Collins Ughalaa, ya ce zargin “marasa tushe ne kuma balle makama”.
Ughalaa ya ce “Abin takaici ne yadda mai magana da yawun tsohon mataimakin gwamnan zai iya yin irin wannan ikirarin mara tushe. Gwamnan baya tsoma baki cikin harkokin ‘yan sanda. Yana mutunta doka.”
“Gwamna ko gwamnatin jihar Imo ba su da hannu a kame tsohon mataimakin gwamnan.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Jirgin Kasa Ya Murkushe Motar Ma’aikatan Gwamnati
Wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba sun jikkata bayan da jirgin fasinja ya murkushe wata motar bas din ma’aikatan gwamnatin jihar Legas a kan hanyarta daga Ikotun zuwa Alausa sakatariyar jihar a yankin PWD na jihar.
Hadarin ya afku ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Alhamis.