Gwamnan jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu Sokoto, ya bayar da umarnin sake gyara gidan tsohon shugaban kasa Shehu Shagari gaba daya da gobara ta kone a makon jiya.
Gwamnan ya bada umarnin ne a ranar Asabar din da ta gabata jim kadan bayan ya ziyarci gidan da ya kone domin tantance irin barnar da gobarar ta yi.
Karanta nanMataimakin Gwamna Obaseki Ya Bayyana Ranar da Zai Ayyana Aniyarsa taTsayawa Takarar Gwamna
Ya bayyana gobarar a matsayin bala’i da ban tausayi, inda ya bayyana gidan da ya kone a matsayin mai tarihi ba wai ga jihar Sakkwato kadai ba har ma da kasa baki daya.
A gare mu, wannan gidan yana da matukar muhimmanci a tarihi kasancewar gidan tsohon zababben shugaban kasa na farko a Najeriya Shehu Usman Aliyu Shagari.
Gwamnatina za ta kasance mai son aje tarihi don haka mun dauki nauyin sake gina wannan gini gaba dayans Insha Allah Aliyu ya tabbatar wa matasan Sokoto.
Kamar abin tarihi ne ga tsararraki masu zuwa, saboda haka, za mu gyara wannan gidan in ji Aliyu.
Yayin da yake jajantawa iyalan marigayi shugaban kasar kan gobarar, Aliyu ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya kiyaye afkuwar lamarin ba tareda an rasa rai ba.
Wasu daga cikin iyalan tsohon shugaban kasar ne suka zagaya da gwamnan yankin da abin ya shafa na gidan da aka kona.
A wani labarin kumaMataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Gana da Wasu Gwmnoni a Ogun, Ya Bukaci Hadin Kan Najeriya
Wadanda suka raka gwamnan a ziyarar sun hada da shugaban jam’iyyar APC na jihar Sen. Aliyu Magatakarda Wamakko, kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto, Rt. Hon. Tukur Bala Bodinga.
Mataimakinsa, Kabiru Kware, Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha, Isa Saddiq Achida, Sakataren Gwamnatin Jiha, Muhammad Bello Sifawa, ‘yan majalisar zartarwa ta jiha, masu ba da shawara na musamman da mataimaka na musamman da dai sauransu.