Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce jami’anta sun cafke wani mutum mai suna Benjamin Ezeukwefor, wanda ake zargi da kitsa zamba tare da damfarar wasu ‘yan Najeriya,inda yace kamfanin Dangote ya masa farashin tirelolin siminti.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana a ranar Lahadi cewa an kama Ezeukwe ne a ranar 19 ga watan Oktoba a unguwar Rumuolumeni da ke karamar hukumar Obio/Akpor a jihar Ribas.
Karanta nanGwamnatin Jahar Sokoto Zata Sake Gina Gidan Shehu Shagari Da Ya Kone
Ya ce kama shi ya biyo bayan tsauraran bincike da jami’an ‘yan sandan “Area A” suka yi a jihar Legas na tsawon makonni.
Hundeyin ya kuma lura cewa ‘yan sanda sun gano abubuwa da dama na bata gari a hannun wanda ake zargin lokacin da aka kama shi.
Hundeyin ya bayyana cewa, Ezeukwe ya kirkiro wani talla na bogi amma mai gamsarwa ta yanar gizo a watan Satumba, wanda Dangote Cement ya yi, inda ya yi ikirarin cewa an yi mas farashin simintin.
Wasu kwastomomi da ba a san ko su wanene ba ne suka fadi yadda suka yi asarar miliyoyin Naira ga wanda ake zargin.
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya aikata wasu zamba a baya tun kafin yanzu kuma can a baya an taba gurfanar da shi a gaban kotuin ji Hundeyin.
A wani labarin kuma
Rashin Kyawon Hanyoyi Yana Taimaka Wa Ta’addanci A Arewa Maso Gabas-Gwamnoni
An bayyana rashin kyawun hanyoyin na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin tsaro da ci gaba a yankin Arewa maso Gabas.
Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da abubuwa 11 da ta fitar a karshen taronta na 9 da ta gudanar a Yola, Jihar Adamawa a ranar Asabar.
Sanarwar da Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya sanya wa hannu, wanda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya karanta, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda yankin ke fama da talauci.