Gwamnatin Jihar Bauchi ta Kaddamar da Ka’idoji na Kasa kan Samar da Kayan Tsarin Iyali da Kudin jiha, a jihar.
Wannan na daga cikin shirin tsarin asusun tallafawa iyali na majalisar dinkin duniya wato United Nations Family Planning Fund.
Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ne ya kaddamar da shirin a gidan gwamnatin Jihar a wannan Litinin.
Sanata Bala Muhammad wanda kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Abubakar Y. Suleiman ya wakilceshi, ya ce wannan shiri zai taimaka matuƙa gaya wajen samar da ingataccen tsarin kiwon lafiya uwa da kuma ɗanta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Mataimakin Gwamna Ya Fice Daga Taro Bayan Hana Hadimin Sa Shiga
Bala Muhammad ya ce lura da irin halin da gwamnatinsa ta samu harkar kiwon lafiya ne a 2019 ya sa ta kafa dokar ta baci a bangaren don farfado dashi.
Cikin abubuwan da gwamnatinsa ta aiwatar don bada gudunmawarta ga tsarin iyali har da samar da kayyakin tsarin iya a kimanin asibitoci 600 a fadin jihar.
Bugu da ƙari ya ce gwamnatinsa ta yi aiki tuƙuru wajen ganin harkar lafiya ta tsaya da kafafunta ta hakanne ma ba tare da wata wata ba daga hawansa mulki zuwa yanzu ya samar da likitoci da unguwan zomomi kimanin 1500 a fadin Jihar gami da gidajen ma’aikatan jinya.
Da ya taɓo ɓangare shelkwatar ƙananan hukumomi da kuma kewayensu kuma, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta gina manya asibitoci wato General Hospital kimanin 26 a kananan hukumomi 20 na fadin jihar, wanda hakan ya saukaka wa al’umma ɗawainiya da suke fama da shi a asibiti.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban hukumar lafiya matakin farko a Jihar Bauchi Dr. Rilwanu Muhammad ya ce a yanzu haka akwai asibitoci kimanin dubu guda dake rarraba kayayyakin tsarin iyali kyauta a jihar wanda gwamnatin jihar ce da hadin gwiwar kungiyoyi da kasashe suka samar.
Dr. Rilwanu Muhammad ya ce a bangaren hukumar da yake jagoranta ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen baiwa mata masu juna biyu kula lura da yadda ake yawan samun mace-mace yayin haihuwa.
A nata ɓangaren kuwa Ko-odinetan asusun tallafawa shirin tsarin iyalin na Majalisar dinkin duniya a Najeriya Misis. Loide Agamko, ta ce wannan an shiryi an tsara kaddamar da shi ne a dukkannin jihohi 36 na fadin kasarnan ciki harda birnin tarayya Abuja da nufin kyautata lafiyar uwa da danta.
Daga sai ta hori malaman addini da ma sarakanun gargajiya da su bada muhimmanci wajen wayar da mabiyansu kai kan abinda ya shafi tsarin iyali da zummar inganta lafiyarsu.