Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana ranar Litinin 1 ga watan Agusta, 2022 a matsayin ranar hutu domin shiga sabuwar shekarar Musulunci, ta watan Muharram 1444 bayan hijira.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban ma’aikatan, Alhaji Safiyanu Garba Bena, kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tattalin Arzikin Jamus Ya Tsaya Cak, Yayin Da Koma Bayan Tattalin Arzikin Kasar Ke Kara Tabarbarewa
A cewar sanarwar, hakan ya biyo bayan ayyana ranar Asabar 30 ga watan Yuli a matsayin 1 ga watan Muharram, wata na farko na sabuwar shekara ta Musulunci.
An sanya ranar Litinin a matsayin ranar hutun domin baiwa al’ummar musulmi damar gudanar da bukukuwan sabuwar shekara ta Musulunci.
A wani labarin Kuma Tsohon Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, da wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of Rights for All International, sun shigar da sammaci a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja suna neman ta ba da umarnin ayyana Nwajiuba a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Sun kuma roki kotun da ta soke kuri’un da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Nwajiuba wanda ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ba da cin hancin ga daliget da daloli ya gabatar da batutuwa 26 domin tantancewa a kotu.
Ya kuma bukaci kotun da ta tantance ko adadin ya ci karo da sashi na 11 (A) 12(1) da 13(1) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
Tsohon ministan ya bukaci kotun da ta tantance ko adadin wakilan da za a yi zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP bai sabawa sashe na 33(1) da (5) (c) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.
Ya roki kotun da ta tantance ko idan aka yi la’akari da bayyananniyar sharuddan da ke tattare da sashe na 6 (6) (A) (B) da (C) da aka karanta tare da sashe na 15 (5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, kotun ta na da ikon shari’a na sokewa, da kuma ayyana zabukan a matsayin haramtattun zabukan fidda gwani na shugaban kasa na APC da PDP.
Nwajiuba ya bukaci kotun da ta tabbatar da cewa duk kuri’un da aka kadawa Tinubu da Atiku a babban taron kasa musamman na jam’iyyun APC da PDP sun sabawa doka, ba su da wani tasiri, kuma ba su da wani amfani a kan dalilan cin hanci da rashawa da sayar da kuri’un daliget don su jefa musu kuri’a.
A karshe ya roki kotun da ta yanke hukuncin cewa, dangane da karin bayani na sakin layi na 1 da na 8 na kundin tsarin mulkin 1999 na 5, zargin cin hanci da rashawa da Tinubu da Atiku ke yi na sayen kuri’u da kuma jawo wakilai da daloli da Naira domin su samu kuri’u a babban taron kasa na musamman, ya hana su ci gaba da neman, tsayawa takara, da rike mukamin shugaban kasa.