Gwamnatin jihar Ogun ta sanar da dage ziyarar aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar wanda aka shirya gudanarwa ranar Talata 21 ga watan Disamba 2021.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Ogun, Tokunbo Talabi ya fitar ranar Juma’a a Abeokuta, gwamnatin ta ce za a sanar da sabuwar ranar ziyarar da kuma kaddamar da wasu muhimman ayyuka na gwamnatin Yariman Dapo Abiodun a lokaci na gaba.
Gwamnati ta yi nadamar duk wani rashin jin dadi da zai iya haifar wa bakin da aka gayyata, in ji sanarwar.