By Abbas Yakubu Yaura
Fitacciyar jaruma a Masana’antar shirya finafinai ta kannywwod Maimuna Muhammad, tace mafi yawan mazan dasu ke zuwa wajen mu da maganar aure bada gaske su ke zuwa ba.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya dangane da kallon da a ke yi musu na cewa su masu ruwan ido ne, wanda Hakan ya ke Hana su yin aure. In data ke cewa
“Wallahi yanzu idan Mace ta biye wa namiji sai ya Kai ta ya baro.Domin bari na fada maka, duk mafi yawan maganar da namiji zai zo yace yana son ka, wallahi karya ce. Sai Mace ta tara samari ko sun Kai dari da wuya ka fitar da guda biyu dasu ke son ka tsakanin su da Allah, sauran duk na banza ne, don haka masoya na gaskiya a yanzu sun yi wahala. “
Daga Karshe ta yi Kira ga ‘yan uwanta Mata dasu yi taka tsan tsan da mazan wannan lokacin domin suna da hatsari.