Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta kashe naira miliyan 25 na biyan kudaden lasisi ga hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa, NBC, wadanda suka tara tun shekarar 2017.
A cewar wata sanarwar manema labarai da kwamishinan yada labarai na jihar, Hon. Ibrahim Magaji Dosara,ya fitar yace Gwamna Bello Mohammed ya ba da izinin biyan hukumar basussukan cikin gaggawa a makon da ya gabata don dakile rufe kafafen yada labarai na jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Bauchi
“Kudaden da aka riga aka biya a asusun hukumar a ranar Juma’ar makon da ya gabata, wani bangare ne na alkawurran da gwamnati ta yi na ci gaba da kyautata huldar aiki da hukumar da sauran kafafen yada labarai domin tabbatar da an sanar da mutane cikkaken shirye-shirye da manufofin gwamnati na ci gaban al’ummar Jiha,” sanarwar ta kara da cewa.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta biya Naira miliyan 5 daga cikin bashin da aka fara bi na Naira miliyan 37 tun bara.
Dosara ya taya al’ummar jihar murnar samun gwamna mai rikon amana irinsa, sannan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da yi wa gwamnan addu’ar Allah ya kara albarka ga jihar.
A wani labarin kuma, Kada Ku Yi Watsi Da Doka Wajen Tara Kuɗaɗen Yakin Neman Zaɓe, FG Tayi Gargadi
Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bukaci ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da kada su ji takaicin cewa ba za su iya kada kuri’a a zaben 2023 ba saboda har yanzu doka ba ta goyi bayansu ba.
A yayin da take shawartar su da su kara kaimi wajen ganin an shigar da Majalisar Wakilan kasashen waje kuri’u a matsayin doka, a ranar Asabar, ta kuma yi gargadi game da saba wa dokokin kasa a kokarinsu na tara kudaden yakin neman zabe domin tallafa wa ‘yan takarar shugaban kasa.