Jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Alh. Alhassan Gambo mai shekaru 60 na Unguwan Bawa a Jihar Kaduna, Badamasi Saadu da Abdullahi Sani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kada Ku Yi Watsi Da Doka Wajen Tara Kuɗaɗen Yakin Neman Zaɓe, FG Tayi Gargadi
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, an kubutar da wadanda harin ya rutsa da su ba tare da jin wani rauni ba, inda suka koma ga iyalansu bayan an duba lafiyarsu.
Ya bayyana cewa, “Wadanda ake zargin ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2022, sun yi garkuwa da Alhassan Gambo na Unguwan Bawa, jihar Kaduna, inda suka harbe wani Alh Mujitafa Usman na karamar hukumar Funtua a jihar Katsina, wanda ya je kasuwa a kauyen Tulu a jihar Bauchi.”
Kakakin ‘yan sandan ya koka da yadda wani dan banga ya biya mafi girman farashi a fafatawar ‘yan banda da jami’in dan sanda reshen Tulu ya jagoranta a yayin da suke tsaka da artabu da masu garkuwa da mutane.
Ya kuma bayyana cewa, a ranar 27 ga watan Agusta, 2022, da misalin karfe 21:00 na safe, wasu bayanan sirri da aka samu a hedikwatar ‘yan sandan Tulu, sun nuna cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare hanyar Tulu-Rishi.
Bayan bin diddigi da kuma sanya ido sosai a yankin a ranar 28 ga watan Agusta, 2022, ya bayyana cewa an kama wasu mutane biyu da aka samu suna yawo a yankin, inda ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano alakarsu ko akasin haka da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Sanarwar ta bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Umar Mamman Sanda ya jajantawa iyalan dan banga da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Ya bayyana cewa wasu gungun ‘yan banga dauke da adduna, wukake, sanduna da sauran muggan makamai a ranar Talatar da ta gabata sun kai hari ga mambobin kwamitin zaman lafiya da tsaro na ofishin Bakin Kura tare da raunata wasu ‘yan kwamitin biyu, wato Danladi Suleiman mai shekaru 32 da Yakubu Ibrahim (42).
A cewarsa, tawagar jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin kwamanda Rapid Response Squad (RRS) sun yi gaggawar kai dauki inda suka yi nasarar cafke wasu maza ashirin da biyu (22) da ake zargi wato Aliyu Adamu mai shekaru 15 na unguwar Bakaro, Ukasha Abubakar na Kofar mukaddas, da Abdulmalik Abdullahi na Kandahar quarters a cikin garin Bauchi.
Sauran sun hada da Nura Inuwa mai shekaru 17 dake unguwar Bakaro, Umar Abdullahi 18 na Malan Goje, Mohammed Mohammed Koli 18, Umar Sulaiman 23, Ibrahim Idris 15, Kabiru Shehu 14, Musa Usman 14, Buhari Sani 18, Aliyu Yakubu alias (Ali luta), Isah Nuhu, Abdulsamat Aliyu, Muhammad Umar alias, Aliyu Adamu Aliyu, Abubakar Adamu, Mujahid Abdullahi (alias (James), Ibrahim Yunusa alias ‘Dan-mama’, Mubarak Ismail wanda ake yi wa lakabi da ‘Dangongo’ da Abdullahi Garba wanda ake yi wa lakabi da (Dan Alhaji).
Ya tabbatar da cewa dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin da aka aikata, inda ya ce kwamishinan ‘yan sanda, CP Umar Mamman Sanda ya bayar da umarnin gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu.
A wani labarin kuma, ‘Yan Boko Haram Sun Kai Hari Masallacin Borno Sun Kashe Limami Da Wasu Mutane Uku
Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a wani masallaci a Borno, inda suka kashe babban limamin Gima da wasu masu ibada uku.
Harin wanda ya afku a ranar Juma’a, ya kuma yi sanadin jikkatar mutane da dama yayin da ‘yan ta’addan suka mamaye al’ummar Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno.