By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta duk wani gudanar da shagulgulan na zamantakewa, bikin aure, wasanni da kuma nishadi a harabar makarantun gwamnati.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi Dakta Yusuf Saleh ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Kaduna.
Saleh yace sun dauki wannan matakin ne domin kare ababen more rayuwa a makarantu daga ‘yan ta’adda.
“An dade ana amfani da wasu makarantunmu wajen gudanar da ayyuka iri-iri, kuma a karshen wannan rana, an lalata kayayyakin makarantar.
“Kowace rana, muna samun koke-koke da bukatu daga ’yan kasa don ginawa, ko gyara wani wuri a makarantu, kuma wannan ya lashe makudan kudade wajen gyarwa.
“Saboda haka, yana da matukar muhimmanci a dauki matakan da suka dace don kare ababen more rayuwa na makarantar kuma wannan yana daya daga cikin irin wadannan matakan,” in ji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa tuni aka aike da sanawar ga daukacin Shugabanni da Manyan Malaman Makarantun Sakandare da na Firamare, inda aka umurce su dasu daina bayar da harabar makarantu domin gudanar da bukukuwa da kuma taron jama’a.
Sannan yace wasu makarantun basu da shinge, yana mai jaddada cewa ana shirin gina shingen a dukkan makarantun jihar.
Sannan ya kara da cewa ma’aikatar tana kuma karfafa hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta cikin gida da harkokin cikin gida da kuma ‘yan banga na jihar Kaduna, domin samar da tsaro da ake bukata a makarantu.
A cewarsa, kokarin zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da suka shafi gudanar da ayyukan wasu makarantun jihar cikin sauki.
Da yake mayar da martani game da ci gaban, Shugaban Jama’a Tijjani Aliyu, ya yabawa gwamnatin jihar bisa amsa kiran da ‘yan kasa suka yi na kare kayayyakin makarantu.
Kazalika yace, KADBEAM, a taron masu ruwa da tsaki kan kalubalen dake fuskantar ilimin ‘ya’ya mata a jihar, ya bukaci gwamnati data samar da mafita mai dorewa kan lalata kayayyakin makarantar.