Gwamnatin Kano ta ce zata tattauna da sauran gwamnonin Arewa kan samar da manhajar karatu ta bai ɗaya ga makarantun tsangaya a shiyyar.
Gwamna Ganduje, wanda mataimakin sa, Nasiru Yusuf Gawuna a daren jiya Alhamis,lokacin da gidauniyar Khalifa dan kaɗai ta gabatar wa gwamnatin sabuwar man hajar karatu ga tsangayun Arewacin Kasar nan.
Ya ce akwai bukatar samar da manhajar karatun bai ɗaya domin kawo gyara a halin da almajirai ke ciki.
Gwamna ya kuma yaba da yadda ƙungiyar tayi aiki da ƙwararru wajen duba darussan da suka dace da karatun tsangaya ba tare da kawar da ilimin da ake samu tun asali ba.
Da yake jawabi tun da fari, Shugaban Gidauniyar, Khalifa Mustapha Dan Kadai ya ce sun ɗauki nauyin samar da manhajar ne ganin bukatar kawo sauyi cikin tsarin ilimin tsangayu.
Ya ƙara da cewa sun kuma ɗauki nauyin tsangayu sittin, wato goma daga kowace jiha domin tallafawa tsangayu.