Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya Amince da daukar sabbin Ma’aikatan hukumar Hisbah 3,100 domin raba su ga shiyyoyin hukumar dake kananan hukumomin Kano 44, da kuma shelkwatar Hukumar dake Sharada.
Babban Kwamandan hukumar Hisbah na Kano Sheik Harun Ibn Sina ne ya bayyana wannan cigaba da hukumar ta samu yau a ofishin sa, dake shelkwatar Hukumar ta jiha.
Sheik Ibn Sina Ya ce kaso 80 cikin dari na wadannan sabbin ma’aikata sun kasance maza ne, yayin da kaso Ashirin suka kasance mata ne.
Ya kara da cewa daga cikin adadin da Gwamna ya amince da daukar su aikin, kaso 70 sun kasance jami’an hukumar ne na sa kai, yayin da kaso 30 suke Sabbi, kuma za a raba su zuwa shiyyar hukumar dake lungu da sako na kananan Hukumomin Kano.
Idan dai za a iya tunawa, a Shekarar data gabata sai da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da daukar Ma’aikatan Hukumar 5,700, wadanda suma yanzu haka ke ci gaba da aiki a sassan hukumar dake Kano daban daban.
A karshe Kwamandan Hukumar ya bukaci daukacin wadanda abun ya shafa da su tuntubi ofishin su na ainihin karamar hukumar da mutum ya fito domin bin mataki na gaba.