Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sake duba karin kashi 50 cikin 100 na alawus-alawus din kudin karatu na ‘yan asalin jihar da ke karatu a makarantun Najeriya da kuma fitar da Naira miliyan 865, 449,150.00 ga hukumar ba da tallafin karatu ta jihar a matsayin fitaccen alawus da kudin kayan karatu don biyan dalibai a fadin kananan hukumomi 44 na masarautu biyar da ke jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya yi wa manema labarai karin haske kan sakamakon taron na mako-mako da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati, Kano, ya bayyana cewa adadin dalibai 40,494 ne za su ci ji gajiyar tallafin.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/kotu-ta-tisa-keyar-tsohuwar-ministar-mozambique-gidan-yari-kan-laifin-almundahana/
Ya kara da cewa, jimillar tallafin karatu ga daliban cikin gida guda 40, 494 daga masarautar Karaye, Bichi, Rano, Kaya da Kano a cikin kananan hukumomi 44 na jihar ya kai Naira 836, 269, 150, yayin da kudin kayan aikin karatu ya kai naira miliyan 29,180, 000.00.
Malam Garba ya ci gaba da cewa masarautar Karaye tana da kananan hukumomi takwas da dalibai 3,094 za su samu kudaden alawus-alawus na Naira miliyan 61,463,950.00 da kuma Naira miliyan 4,020, 000.00 a matsayin kudin karatun, yayin da masarautar Bichi mai kananan hukumomi tara da dalibai 3,494 za su samu Naira miliyan 71,242, 800.00 a matsayin manyan alawus da kuma Naira miliyan 4,020.000.00 na kayan aiki.
Kwamishinan ya kuma zayyana alawus-alawus da kayan aiki ga dalibai 4,015 daga Masarautar Rano maai kananan hukumomi 10 sun kai Naira miliyan 78, 351, 800.00 da Naira miliyan 4, 02, 000.00, sai Masarautar Gaya mai kananan hukumomi tara da dalibai 4, 260 ne za su karbi Naira miliyan 86, 236, 600.00 a matsayin alawus alawus da kuma Naira miliyan 4, 02, 000.00 na kayan aikin karatu.
Masarautar Kano, ya ce, tana da kananan hukumomi takwas na da fitattun alawus-alawus ga dalibai 26, 086, kuma za su karbi Naira miliyan 538, 974, 000.00 da kuma biyan Naira miliyan 13, 100, 000.00 na kayan aikin karatun.