Duba da kalubalen tsaro da ake fama da dashi, tare da cunkoson makarantu da ke wajen birnin, gwamnatin jihar Kano ta fara soke kadarorin da aka mallaka da Basu da rajistan domin kafa manyan makarantun sakandare.
Matakin na da nufin rage yawan makarantun kwana a fadin kananan hukumomi 36 dake jihar, biyo bayan garkuwa da dalibai da ake Samu a wasu makarantun kwana a jihohin makwabta.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya bai wa manema labarai a Kano ranar Litinin.
Ya ce yayin da a halin yanzu gwamnati ke bitar yanayin da Kuma kokarin dakile hare -hare kan yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran masu aikata laifuka a dazukan da ke makwabtaka da jihar, gwamnati za ta tashi tsaye wajen daukar matakan da za su tabbatar da tsaron makarantun a fadin jihar Kano.
Malam Garba ya ba da misali da daya daga cikin irin waɗannan abubuwan da aka ƙwace kuma aka canza su, kamar Filin Bola dake kan Titin Court, a ƙaramar hukumar Tarauni dake jihar, wanda ba shi da izinin ginin, inda gwamnati za ta kafa katafariyar makaranta.
Ya ce makarantar zata kunshi ajujuwa guda 18, katafaren dakin gwaje-gwaje, Babban dakin Taro, sahsin hukumar gudanarwar Makarantar, filin wasanni, bandaki na musamman, da dai sauran su.
Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa, gwamnati ta lura da cunkoson daliklbai da ake Samu, dake haifar da yanayin maras dadi, a fannin harkokin makarantun.
Har’ila yau ya kuma bayyana cewa, gwamnati ka’iya kuma kwace kadarorin da aka gina su, a yankunan da aka ware domin wata manufa ta daban.
A karshe Malam Garba ya yi nuni da cewa, a halin yanzu gwamnati “tana duba lamuran filaye da amince da su domin al’uma, amma a ka juya su zuwa shaguna ko wuraren kasuwanci, wanda a yanzu ake kokarin Mai da komai zuwa Muhallin sa.”