Gwamnatin Kano ta ce karar fashewar da akaji a yankin unguwar sabon Gari dake karamar hukumar Fagge, ba Bom bane kamar yadda ake ta yaɗawa.
Kwamishinan yada labarai na Kano Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a wata Sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannunsa, a yau Litinin, inda yace Tukunyar Gas ce ta fashe, a wani shagon siyar da abincin dabbobi daura da wata makaranta a akan titin Aba Road.
Ya Kara da cewa yanzu haka jami’an tsaro na ci gaba da bincike akan fashewar Tukunyar Gas, amma dai yanzu a matsayin su na Gwamnati ba su samu rahoton kan musabbabin fashewar gas ɗin ba.
Lamarin dai ya faru ne a yau Litinin, wanda ya sanya fargaba da zullumina zukatan mazauna yankin, wanda kuma tuni jami’an tsaro suka shinge wajen da lamarin ya faru.
Kazalika Kwamishinan yan Sanda na Kano CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya halarci wajen da inda shima ya tabbatar da cewa ba Bom bane ya fashe, Tukunyar Gas ce.