An samu barkewar wani hayaniya a Tripoli Babban Birnin kasar Libya.
Mambobin Yan aware daga Gabashin kasar sun farwa garin ne da daddare awani yunkuri na karbe Iko da kasar.
Sun Kuma bar Babban Birnin awanni kadan bayan fafatawar.
Yan awaren dauke da makamai sun raka Fathi Bashagha, Faraministan da Yan Majalissar Dokokin Gabashin libiya suka nada a matsayin Faraministan da suka amince da shi.
Fathi Bashagha yayi kokarin karbe Ikon kasar ne daga abokin hamayyarsa Abdulmajid Al-Dbeibah, Wanda aka nadashi amatsayin Faraministan Libiya tun bayannan tattaunawar zaman lafiya da majalissar Dinkin duniya ta jagoranta.
Mr Mashagah na zargin Al-Dbeibah da shiga Ofishin Faraministan kasar batare da gudanar da zabe ba kamar yadda aka tsara a baya.