Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sakin naira miliyan dari uku (N300,000,000) a matsayin kudin karatu ga daliban jihar Kano da aka dauki nauyin karatu su a jami’ar Near East University dake kasar Cyprus.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano, Sanusi Abdullahi Kofar Na’isa ya fitar a ranar Juma’a.
KARANTA KUMA Gwamnatin Kano Ta Amince Da KarinnKashi 50 Na Tallafin Karatun Daliban Jihar
Sanarwar ta ce an ci gaba da samun ci gaba a kokarin gwamnatin jihar na inganta karfafawa matasa ta hanyar samar da ingantaccen ilimi.
A cewar sanarwar, kwamishiniyar ilimi mai zurfi Dr. Mariya Mahmud Bunkure, ta bayyana cewa biyan bashin yana cikin alkawarin da Gwamna Ganduje ya yi na daga darajar zamantakewa da tattalin arziki na hadakar matasan jihar ta hanyar samar da ingantaccen ilimi a kuma lokacin da ya dace.
“Kwamishiniyar ta godewa gwamna bisa ganin wannan mafarkin ya tabbata”,
‘’ Daga nan sai ta yi amfani da wannan damar wajen taya daliban da iyayensu murnar samun irin wannan gagarumin tallafi, inda ta jaddada bukatar yin amfani da ilimin da aka samu wajen ci gaban jihar Kano da ma Najeriya baki daya’’.
A Wani Labarin Kuma Zan Sake Gina Najeriya – Dan Takarar Shugaban Kasa
An dakatar da harkokin kasuwanci da zirga-zirgar ababen hawa a ranar Juma’a a Benin, biyo bayan dimbin jama’a da suka yi dafifi a kan tituna daban-daban domin tarbar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi.
Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a filin taro na Baptist, wurin taron gangamin shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Obi ya yi alkawarin sake gina kasar idan aka zabe shi.