Gwamnatin jihar Kano tayi alkawarin Kara kulawa da makarantun Islamiyya dama karatun na Islamiyya a fadin jihar.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shine yayi wannan alwashi lokacin daya halarci saukar karatun Alqur’ani mai girma na dalibai 232 na makarantar babban malami na Madabo da akayi a makarantar sakandire ta Gwammaja.
Gwamna Ganduje yace, la’akari da tarihin makarantar na fiyeda shekaru 60 yasanya a shekaru uku da suka gabata gwamnati ta tallafa aka fara kokarin Samar da mazauni na dindindin ga makarantar.
Gwamnan yayi alkawarin tallafin Naira miliyan 10 domin cigaba da ginin makarantar bayaga Naira dubu 500 daya baiwa malaman makarantar bisa kokarin su na tarbiyyar ‘ya’yan musulmi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan ma’aikatar kula da al’amuran addinai Dr Muhammad Tahar Adamu Baba impossible da kwamishinonin ilimi dana muhalli.
Comments 1