Gwamnatin Kano za ta kashe Naira Biliyan 8 wajen gina Makarantun Firamare guda uku
Gwamnatin Jihar Kano ta ware Naira biliyan 8 domin gina manyan makarantun firamare guda uku a fadin jihar.
A cewar Gwamnan Jihar Abba Yusuf, Makarantun za su kasance da cikakkun kayan aikin koyarwa da za su samar da isasshen yanayin koyo da koyarwa mai kyau ga yara marasa galihu domin samun ingantaccen ilimi domin samun ci gaba a nan gaba.
Gwamnan ya ce za a kafa makarantun ne a kowace mazabar Majalisar dattawa, sannan za a samar da kayayyakin koyo na zamani don samar da ilimi mai inganci a matakin farko Firamare.
Ya kuma ce an ware Naira biliyan 6 domin gyara dukkan makarantun firamaren da ke faɗin Jihar.
Hakazalika ya ce, Gwamnati ta amince da gyara wasu Makarantu na musamman guda 26 da tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ya kirkiro yayin da yanzu haka aka kammala guda 17.
KARANTA NAN:Gwamnatin Oyo Ta Yi Kiran A Kwantar Da Hankula Kan Wata Fashewa Da ta Afku
“Zamanin da yara ke ɗaukar darasi zube a ƙasa ya wuce” inji Gwamnan.
Za mu ci gaba da ba da kulawa da samar da kayan aikin koyarwa na yau da kullum, wanda hakan zai ba wa yaranmu damar samun kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.
Mun kuma kashe Naira miliyan 500 wajen gina ɗakin kwanan ɗalibai a Jami’ar Aliko da ke Wudil, sannan mun biya Naira miliyan 150 ga sabon sashen kula da muhalli da yanayi na Jami’ar Maitama Sule.
Haka kuma mun biya Naira miliyan 500 ga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar don yin sabbin kwasa-kwasai a Jami’ar Wudil da Yusuf Maitama Sule.
Har ila yau, Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Kano da sauran cibiyoyi sun ci gajiyar biyan sama da Naira miliyan 100 domin yi musu rijistar sabbin kwasa-kwasansu.
Kimanin kashi 93 cikin 100 na kudaden karatun dalibai 501 da karatun digiri na biyu a Indiya da sauran kasashen waje mun biya su, kuma mun biya alawus din su na watanni hudu don ba su damar fuskantar karatunsu yadda ya kamata.
Gwamnan jihar ya kuma ce Gwamnati ta biya Naira miliyan 700 a matsayin kudin rijista ga daliban jihar Kano da ke karatu a Jami’ar Bayero Kano sannan kuma ta biya Naira biliyan 15 a matsayin kuɗin Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) da Jarrabawar NECO ga daliban Jihar (NAN).