Gwamnatin jihar Kebbi ta hannun hukumar dakile yaduwar cututtuka ta jihar, ta tabbatar da mutuwar akalla Mutum 146 a jihar, biyo bayan barkewar cutar kwalara a shekarar nan.
Sakataran Ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Dakta Aminun Haliru Bunza ne ya bayyana hakan, lokacin da ya ke gana wa da Gwamnan jihar Atiku Bagudu da Mataimakin shi Kanar Sama’ila Yombe Dabai mai ritaya a jiya Alhamis.
Inda Kwamishina kiwon lafiyar jihar ya ke bayyana cewa, an Sami rahoton bullar cutar guda 2,208 daga watan Janairun shekarar nan, zuwa watan nan da muke ciki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na zama Yar fim, na kanyi abun da nake so, inji Hauwa
Ya ce “Daga watan Janairun zuwa Ogustan shekarar 2021, mun sami rahoton Amai da Gudawa sau 2,208 a kananan hukumomi 20 dake jihar, inda aka a baya-bayan nan, aka gwada 55, a kasami Mutum 26 dauke da cutar.” A cewar shi.
“Mutum 146 ne muka sami rahoton mutuwar su sanadiyar cutar a fadin jihar, inda Hukumar dakile yaduwar cututtuka a jihar ta tabbatar da barkewar cutar kwalara a jihar.” Inji shi.
A karshe ya bukaci Al’uma da su dauki matakan Kari, da ya hadar da tsabtar jiki, kaucewa bayan gida a bainar jama’a, domin kare kansu da kamu wa da cutar. da kuma dakile yaduwar cutar a fadin jihar.