Gwamnatin Kogi Ta Hana Haƙar Ma’adanai
Gwamnatin jihar Kogi ta haramta haƙo Ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Jihar.
Umurnin ya biyo bayan mutuwar wasu mutane biyu ne a wani wurin hakar ma’adinai a Ika-Ogboyaga a karamar hukumar Ankpa ta jihar a lokacin da wani kaso na ma’adinan ya fado.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Na Shirin Ciyo Bashin Naira Tiriliyan 11 a 2023
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda mutanen yankin suka bayyana sunayensu da Attah da Amodu.
Wani ganau ya ce mutanen yankin da suka samu labarin, sun garzaya zuwa wurin, amma kawai suka kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa, tare da binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kwamishinan ma’adanai da albarkatun kasa na jihar Kogi, Bashiru Gegu, ya ce daga yanzu ya kamata duk ma’aikata su yi rajista da ma’aikatar domin tantance masu hakar ma’adanai na gaske.
Sanarwar ta ce, rashin bin wannan umarni, gwamnatin jihar za ta kama masu aikin hakar ma’adinai da wuraren.
A halin da ake ciki kuma, hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC ta ce ta fara gudanar da bincike domin gano wanda ya mallaki wurin da ya rufta.
Shugaban ma’adanai na rundunar DCC Nkom Samson Katung, ya ce an umurci jami’an sashen da su hada kai da mai riƙe da Sarautar yankin domin dakatar da ayyukan da suka saɓa wa doka a yankin.
A wani labarin kuma: An Kama Ɗan Shekara 22 Da Sace Matashi A Lagos
An kama wani Matashi dan shekara 22 mai suna Ayomide Fawehinmi a ranar Litinin, bisa yunkurin sace wani Matashi a unguwar Empire da kw Surulere, Legas.
Wanda ake zargin wasu Fusatattun Mutane ne suka kusa kashe shi a lokacin da aka fara ganin sa tare da wanda aka sace.