Gwamnatin Lagos ta Ƙaddamar da Hukumar Hana Sana’ar Acaɓa
Gwamnatin Jahar Lagos ta Ƙaddamar da Hukumar Hana Acaɓa, domin marawa ƙoƙarin Yan Sanda baya, wajen hana Okada a saman daBabura a faɗin Ƙananan Hukumomi 6 a manyan hanyoyi, da Gadoji.
Kwamishinan Sufuri Dr. Frederick Oladeinde ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Talata daya fitar a Lagos, yace hana Acaɓa yayi dai-dai da Dokar Sufuri, Doka ta 2 ta Shekarar 2018.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗuminsa: Gobara ta kama a Rukunin wasu Gidaje a Ikoyi
Oladeinde yace Gwamnati a shirye take ta sanya Dokar hana zirga-zirgar Ababen hawa a faɗin Ƙananan Hukumomi 6 da Cibiyoyin Cigaba na Yankin.
Kwamishinan yace a bikin kaddamar da Hukumar, yace Hukumar Hana Acaɓa zata riƙa kaiwa ga Ƴan Sanda.
Oladeinde yayi kira ga ƴan ƙasa dasu haɗa hannu da Gwamnati.
“Hakƙi ne akan Al’umma sukai rahoton duk wani abu da aka yi masu na rashin adalci ga Ma’aikatar Sufuri.
“Al’umma zasu iya kai rahoto ta wannan layukan 09038208154, 09034810153, 09033090826, da kuma 09169655855.
Comments 1