Gwamnatin jihar Legas ta umurci dukkan manyan masu sayar da man fetur masu zaman kansu da ke aiki a kan manyan tituna a jihar da su bude tsakanin karfe 9 na safe zuwa 4 na yamma a ranakun mako.
Gwamnati ta yi gargadin duk wani ma’aikacin da ya ki bin umarnin daga yanzu za a saka masa takunkumi mai tsanani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Amincewa NNPC Ya Kashe Naira Tiriliyan 1.9trn Wajen Ayyukan Gina Tituna
Umurnin, a cewar gwamnati, shi ne don taimakawa wajen rage tasirin ayyukansu a kan yanayin zirga-zirgar, wanda ke ci gaba da tabarbarewa yayin da karancin kayan masarufi ke daurewa.
Kwamishinan Sufuri na jihar Legas Dr Frederic Oladeinde ya umurci duk gidajen mai masu zaman kansu da kuma manyan masu sayar da mai da ke da gidajen sayar da man Fetur a kan manyan tituna a cikin babban birnin Legas da su bi umarnin.
Oladeinde ya ce dokar ta karfe tara na safe zuwa karfe 4 na yamma za ta ci gaba da aiki har sai an shawo kan matsalar karancin man fetur.
Ya kara da cewa an bukaci hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) da hukumar duba ababen hawa (VIS) da sashin kula da zirga-zirgar ababen hawa (TOCU) da sauran hukumomin tabbatar da doka da oda domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa a fadin jihar.
Ya gargadi duk manyan gidajen mai masu sayar da man fetur masu zaman kansu da su bi wannan umarni ko kuma a sanya musu takunkumi.
A wani labarin kuma, CBN Ya Yi Kakkausan Gargadi ga Bankuna Kan Sa Tsoffin Kudi A Na’urar ATM
Babban bankin Najeriya, CBN, ya yi gargadin illar da bankunan kasuwanci za su fuskanta idan aka samu suna sanya tsofaffin katunan kudi a ATM dinsu kafin ranar 31 ga watan Janairu.
Da take magana a ranar Alhamis a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, a lokacin da ake wayar da kan ‘yan kasuwa game da sake fasalin kudin naira, mataimakiyar darakta a hukumar kula da kudaden, Dr Rekiyat Yusuf, ta ce duk wani ATM da aka samu har yanzu an saka masa tsofaffin takardun kudi za a rufe shi kuma a sanya masa takunkumin da ya dace a bankin aiki.