Gwamnatin Legas Ta Fara Wani Yunkurin Samar Wa Marasa Aikin Yi
Gwamnatin jihar Legas ta sake tabbatar da cewa ta samar da tsare-tsare da ke da nufin ganin matasan jihar sun zama masu dogaro da kai.
Babbar Sakatariyar ma’aikatar matasa da ci gaban al’umma Toyin Oke-Osanyintolu ce ta sanar da hakan yayin da take ƙaddamar da bude shirin horar da ‘yan kasuwa mai taken “Business Amplifier Clinic” horon kwanaki 3 ga zababbun matasa ‘yan kasuwa a matsayin wani bangare na shirin samar da ayyuka don bikin ranar Matasa ta Duniya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Juyin Mulkin Nijar: Har Yanzu Tinubu Bai Bada Umarnin Amfani Da Soji Ba – Fadar Shugaban Kasa
A cewar Oke-Osanyintolu, an shirya shirin horas da ‘yan kasuwa matasa ne domin gina sana’o’in matasa da kuma karfinsu.
Wannan, in ji ta, zai karfafa matasa masu tasowa na kasuwanci, jagoranci, da kuma samun basirar da za su taimaka wa mahalarta su dai-dai ta ayyukansu, da matakai don tallafawa sauyin yanayi da abubuwan da suka shafi muhalli.”
Ta kara da cewa ajandar Themes Plus na wannan gwamnati na da burin ganin ba a bar kowa a baya ba. Don haka gwamnati ta ba da gudummawa sosai wajen inganta sana’o’i da koyar da sana’o’in hannu a matsayin babban makami wajen magance matsalar rashin aikin yi na matasa a jihar.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Najeriya Ta Baiwa Sanatoci Kudin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur-Akpabio
Fadar shugaban kasar ta dage cewa shugaba Bola Tinubu bai yanke hukuncin tsoma baki ta hanyar amfani da soja a jamhuriyar Nijar ba yana mai gargadin cewa ba za a lamunta da ra’ayin addini da kabilanci wajen magance hatsarin da ke tattare da durkusar da mulkin dimokuradiyya a kasar Jamhuriyar Nijar da ke yammacin Afirka ba.
Shugaba Tinubu wanda ya umarci Babban Bankin Najeriya, CBN, da ya sanya takunkumin kudi a kan daidaikun mutane da hukumomin da ke da alaka da mulkin soja a Nijar.