Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa shi da abokan aikinsa sun karbi wasu kudi daga majalisar dokokin kasar domin rage radadin cire tallafin mai a daidai lokacin da zasu tafi Hutu.
Labarin samun alawus na jin dafi da walwala ga Sanatoci a cikin wannan yanayin na tabarbarewar tattalin arziki da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur ya baiwa ‘yan Najeriya da dama mamaki.
Inda wasu ke ganin cewar duk da yanayin da kasar ke ciki har yanzu masu kudi kawai ake azurtawa inda shi kuma talaka yake cigaba da dandana kudarsa.
Akwai jita-jita cewa shugaban majalisar dattawan bai san cewa ana daukar bidiyo kai tsaye a gidan talbijin na NTA ba.
KARANTA NANAbinda Muka Tattauna Da Shugaba Tinubu-Okonjo Iweala
A lokacin da yake bayyana cewa an aika wa Sanatoci kudaden jin dadin da aka ce an aike musu ne don hutun su.
A cikin wani faifan bidiyo da DAILY POST ta gani, shugaban majalisar dattawan ya janye maganarsa bayan ya gano cewa ana daukarsa bidiyo kai tsaye.
An dauko bidiyon Akpabio yana cewa “da zaran Sanata Umahi ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin ministan gwamnatin tarayya, za mu sake gyara nade naden da muke cigaba da yi a majalisar dattawa
Sannan kuma domin ba mu damar jin dadin hutunmu, magatakardan majalisar dokokin kasar ya aika da wasu kudade zuwa ga asusunmu daban-daban,” inji shi.
Bayan cire tallafin man fetur a watan Yuni, talakawa na fama da tashin gwauron zabi na sufuri da kayayyaki da kuma ayyuka.
Inda wasu ke bayyana cewar a wuni suna kashe fiye da abinda suke samu wajen zuwa wajen aiki ko kuma kasuwanci.
A WANI LABARIN KUMA
Zamu Yake Ku Idan Kuka Tunzuramu-Amurka Ga Kasar Nijar
Kasar Amurka tayi gargadin cewar hawainiyar kasar Nijar ta kiyayi ramarta idan ko ba haka ba Amurka na gab da kaddamar da yaki akan kasar ta yammacin Afirika