By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Ondo ta rufe asibitoci masu zaman kansu guda goma sha biyar da dakunan wuraren shan magani a gundumar sanatan kudancin jihar bisa zargin ayyukan su ba bisa ka’ida ba da kuma da rashin ingantun kayan aiki.
An kuma kama masu aikin cibiyoyin kiwon lafiya guda goma sha biyar tare da tsare su a ofishin ‘yan sanda bisa zarginsu da gudanar da asibitoci masu zaman kansu a kasa da ka’idojin da ake bukata.
Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar, Folukemi Aladenola, wanda ya bayyana hakan, yace an cafke wadanda ake zargin ne bayan da suka ziyarci cibiyoyin kiwon lafiya 36 da ke Ore, Odigbo, Okitipupa, Ilutitun, da Iju-Odo da sauransu tare da yin kamun.
Shima da yake magana, Shugaban tawagar sa ido kuma Darakta, kula da Asibiti a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Ayodele Adelusi, yace duk wuraren da abin ya shafa baza su sake budewa ba har sai an cika sharudan da ake bukata.