By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya saki zunzurutun kudi har naira miliyan 300 domin biyan basussukan fansho na ma’aikata guda dubu 1,501.
Wata sanarwa da shugaban ma’aikatan, Destus Oyebade ya sanya wa hannu a ranar Litinin din da ta gabata, ta ce kudaden sun kasance a gefe na kudin da aka kayyade na Naira miliyan 508,000,000 da aka amince da su na biyan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da kuma karin Naira miliyan 150,000,000 da aka amince da su don biyan wadanda suka yi ritaya. karkashin tsarin fansho na ba da gudummawa.
Oyebade, ya kuma ba da tabbacin gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata jin dadin ma’aikata da masu ritaya a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, a wani bangare na kudirinsa na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan jihar da suka yi ritaya, ya saki zunzurutun kudi har Naira miliyan 300 domin biyan bashin fansho ga ma’aikata dubu 1,501. .
An saka sunayen wadanda suka yi ritaya a allon sanarwa na ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a, ofishin fansho na jiha,da ofishin fansho na kananan hukumomi da kuma ofishin shugaban ma’aikata.sannan”Biyan wanda aka zaba ya fara aiki daga ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.”