Gwamnatin jihar Ondo ta ce dole ko wani ma’aikaci a jihar yayi allurar riga-kafi Cutar Corona, kafin ranar 1 ga watan Nuwamban Shekarar nan, ko kuma a rufe ofisoshinsu.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar Mista Donald Ojogo ne ya bayyana hakan, a wani taro da shugabanni da daukacin ma’aikatan ma’aikatar kan wa’adin da aka bai wa ma’aikatan jihar, na yin allurar riga-kafin Corona kafin ranar 1 ga Nuwamban Shekarar 2021.
Kwamishinan, wanda ya yi magana ta bakin babban sakatare na ma’aikatar, Mista Adeyemi Adeyemo, ya jaddada cewa, Riga-kafin Bai da wata Illa Kuma yana taimakawa wajen dakile yaduwar cutar ta COVID-19.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yan jarida sun gudanar da Zanga-Zanga a Abuja
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya saki zunzurutun kudi har naira miliyan 300 domin biyan basussukan fansho na ma’aikata guda dubu 1,501.
Wata sanarwa da shugaban ma’aikatan, Destus Oyebade ya sanya wa hannu a ranar Litinin din da ta gabata, ta ce kudaden sun kasance a gefe na kudin da aka kayyade na Naira miliyan 508,000,000 da aka amince da su na biyan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da kuma karin Naira miliyan 150,000,000 da aka amince da su don biyan wadanda suka yi ritaya. karkashin tsarin fansho na ba da gudummawa.
Oyebade, ya kuma ba da tabbacin gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata jin dadin ma’aikata da masu ritaya a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, a wani bangare na kudirinsa na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan jihar da suka yi ritaya, ya saki zunzurutun kudi har Naira miliyan 300 domin biyan bashin fansho ga ma’aikata dubu 1,501.
An saka sunayen wadanda suka yi ritaya a allon sanarwa na ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a, ofishin fansho na jiha,da ofishin fansho na kananan hukumomi da kuma ofishin shugaban ma’aikata.sannan”Biyan wanda aka zaba ya fara aiki daga ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.”