By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Lahadin data gabata ne rahotanni suka bayyana cewa an samu tashin gobara a unguwar Tsamiya Babba dake karamar hukumar Gezawa jihar kano.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gobarar dai ta barke da misalin karfe 18:26 na yamma a wani Kango dake yankin na Unguwar ta Tsamiya Babba wanda ake amfani dashi wajen sarrafa man Inji a cikin sa, baya da haka kuma a kawai wani rami a cikin sa wanda yake dauke da Mai kimanin Lita 10,000 tare da wata tankar Mai wanda take dauke da lamba DJW 111 XA a wajen lokacin da gobarar ta tashi.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar kano Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar mana da faruwar lamarin inda yace sun sami kiran gaggawa ta bakin wani mai suna Tasi’u Abubakar da misalin karfe 6:26 na yamma.
Kazalika Saminu yace gabarar ta rutsa da wasu mutane biyu Baba Azare da kuma wani Ibrahim Bakoro an samu na sarar kubutar dasu da ransu, amma gobarar ta kone tankar man dakuma wajen baki daya.
Sai dai Saminu bai bayyana mana mu sabbabin tashin gobarar ba, inda ya kara da cewa jami’an su na runduna ta 13 daga sakatariyar Audu Bako da kuma jami’an su na runduna ta 26 dake Danladi na Sidi sun sami nasarar kashe gobarar.