Gwmanatin tarayya ta yi kira ga masu zanga -zangar na Manyan motoci a kan babban hanyar Bida zuwa Lambata, da su fahimci cewa haryanzu ana cigaba da aikin gyaran hanyar ne
Daraktan Hulda da jama’a na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje Boade Akinola ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da fitar.
A cewar sanarwar, Babban Sakataren Ma’aikatar Babangida Hussaini ya ce, yanayin aikin bai Kai ga Direbobin su tayar da hankulan su ba, tunda tuni aka umarci Dan kwangilar dake aikin daya yi hanzarin gyara inda hanyar tai matukar lalacewa.
Hussaini ya kara da cewa, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na cigaba da Maida hankali wajan samar da hanyoyin ababen hawa a dukkannin fadin kasar nan. Domin inganta rayuwar al’uma da kuma Bunkasa tattalin arzikin jami’ar Nigeria.
Idan za’a iya tunawa, direbobin manyan motoci sun rufe hanyar Bida zuwa Lambata ne, a ranar Juma’ar data gabata. saboda tsananin lalacewar hanyar wacce ta hada yankin Arewa zuwa Kudancin kasar nan.
Comments 1