Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 6.31 daga babban bankin Kasa CBN domin cigaban al’umma a cikin watanni 10.
Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta yo rancen kudi daga CBN daga Naira tiriliyan 17.46 a watan Disambar 2021 zuwa Naira tiriliyan 23.77 a watan Oktoban 2022.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Naira tiriliyan 23.77 da gwamnatin tarayya ta ciyo a bankin ba ya cikin jimillar bashin da ake bin kasar, wanda ya kai Naira tiriliyan 42.84 a watan Yunin 2022, kamar yadda ofishin kula da basussuka ya bayyana.
KARANTA KUMA Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Bashin Kudi Mara Ruwa Ga Wasu Yan Kasuwa
Bashin da ake binta ya hada da basussukan gwamnatin tarayyar da gwamnatocin jihohi 36, da na babban birnin tarayya.
Ways and Means Advances wani wurin ba da lamuni ne wanda CBN ke biyan gibin kasafin kudin gwamnati.
A cewar sashe na 38 na dokar CBN na 2007, babban bankin na iya baiwa gwamnatin tarayya ci gaba na wucin gadi dangane da gazawar kudaden shiga na kasafin kudi na wucin gadi a irin wannan kudin ruwa kamar yadda bankin zai iya tantancewa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Dokar ta kara da cewa, “Jimillar kudaden ci gaban da aka samu a kowane lokaci ba zai wuce kashi biyar cikin dari na ainihin kudaden shigar gwamnatin tarayya na shekarar da ta gabata ba.
A Wani Labarin Kuma Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Masu Tafiya Kasashen Turai
Gwamnatin Tarayya ta shawarci ‘yan Najeriya da ke tafiya zuwa kasashen Amurka da Birtaniya da wasu kasashen Turai da su yi hattara da barayin da ke kai wa fasfo da kudadensu da wasu kayayyaki masu muhimmanci wawa.
Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed, ya ba da wannan shawarar a ranar Litinin a Abuja yayin da yake jawabi a karo na biyar na makin shugabanci Buhari a 2015-2023.