Gwamnatin Tarayya ta dage cewa ba za ta biya malaman makaranta albashin aikin da ba su yi ba daidai da manufar ‘Ba aiki ba biya’.
Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tsokaci kan zanga-zangar da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi kan biyan rabin albashin watan Oktoba.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Kungiyar ASUU da ta fara yajin aikin a watan Fabrairu, ta janye yajin aikin ne tun a watan Oktoba bayan da Honarabul Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya shiga tsakani.
KARANTA KUMA ASUU Ta Bukaci Ministocin Ilimi Da kwadago SuGaggauta Sauka Da Mukaminsu
Sai dai ‘ya’yan kungiyar sun samu rabin albashi a karshen watan Oktoba, matakin da bai yiwa malaman jami’ar dadi ba.
A ranar Larabar nan ne ‘yan jaridun fadar shugaban kasa suka tattauna ministan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A martanin da ya mayar, Adamu ya ce matsayin gwamnatin tarayya shi ne “ba za a biya Malaman albashin aikin da ba a yi ba.”
Ministan ya kuma mayar da martani game da zargin da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodoke ya yi na cewa biyan malaman makaranta albashin wata dabara ce ta sanya su zama ma’aikatan wucin gadi.
“Babu wanda zai iya sanya malaman Jami’o’i su zama ma’aikatan wucin gadi,” in ji shi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Da aka shaida masa lshirin malaman na barazanar daukar matakin zanga-zangar kwana daya don nuna rashin amincewarsu da matakin da gwamnati ta dauka, Adamu ya ce bai san suna yi ba.
A Wani Labarin Kuma Hukumar EFCC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Canjin Kudade Ba Bisa Ka’ida Ba
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kama wani da ake zargi da canji kudaden ketare ba bisa Ka’ida ba, Mustapha Muhammed wanda aka fi sani da Muaspaha Naira a Abuja.
EFCC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba sannan ta kuma fitar da hoton wanda ake zargin.